Shugaba Jonathan da wasu iyayen 'yanmatan Chibok
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Matakan sako yan matan Chibok

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Jonathan da wasu iyayen yanmatan Chibok

A makon nan ne a karon farko shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, yayi wata ganawa da iyayen 'yan matan da 'yan kungiyar Boko Haram suka sace daga makarantar Chibok na jihar Borno. Wadanne matakai ya kamata a dauka don sako su tunda gwamnati tace tana kokari na ganin an kubutar da su? Abinda zamu tattauna kenan a filin Ra'ayi Riga!