Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gani Mani Hanya 26/07/14

Yayin da hukumomin Najeriya ke cewa suna iya bakin kokarinsu domin kawo karshen ayyukan kungiyar Boko Haram, wani batu da ke tayar da hankali kuma shi ne batun sace mata da kungiyar ke yi.

A watan Mayun da ya gabata ne wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka sace mata da yara kimanin sittin a wasu kauyuka bakwai na jihar Borno kuma har yanzu babu duriyar da dama daga cikinsu.

Hakan ya faru ne bayan sace 'yan mata fiye 200 na Chibok da kungiyar ta yi a watan Afrilu, wadanda suma har yanzu hukumomin kasar ba su kai ga ceto su ba.

Habiba Adamu ta hada mana rahoto na musamman game da halin da irin wadannan mata suka tsinci kansu.