Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Bayanai game da taro kan cutar Ebola a Guinea

Shugabannin kasashen yammacin Africa da ke fama da cutar Ebola za su hadu da hukumar lafiya ta duniya WHO a Guinea.

Taron na kwana guda zai kaddamar da tallafin dala miliyan dari domin yakar cutar Ebola da ta yi sanadiyyar rasa rayukan mutane fiye da dari bakwai a kasashen Guinea, da Liberia da kuma Salo daga watan Fabrairu wannan shekara zuwa yanzu.

Aichatou Moussa ta tattauna da Editan BBC Hausa, Mansur Liman kan mahimmancin taron