Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Taba Kidi Taba Karatu 03/08/14

Kungiyar bunkusa tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma, wato ECOWAS ko CEDAO na aiwatar da wasu manufofi na bai-daya da suka shafi zamantakewa da tattalin arziki, ciki har da ba da 'yancin zirga-zirga ga al'umomin da ke shiyyar. Sai dai alamu na nuna cewa har yanzu ana fuskantar matsala ta fuskar sufuri a wasu sassan shiyyar sakamakon zargin da ake yi na matsalar cin hanci.

Dr Aliyu Tilde fitaccen marubuci ne da kan yi sharhi a kan al'amura a Najeriya, wanda kuma ya kewaya wasu daga cikin kasashen Afirka ta yamma da mota, ciki har da Ghana da Benin, da Burkina-Faso, Togo da kuma Niger da nufin nazarin irin kalubalen da masu yawon-bude a shiyyar ke fuskanta.

Kuma a filinmu na gane-mani-hanya na wannan makon za mu kawo muku tattaunawar da wakilinmu a Yamai, Baro Arzika ya yi Dr Aliyu Tilde lokacin da ya isa Jumhuriyar, inda ya tambaye shi irin abubuwan da ya ci karo da su a ziyarce-ziyarcen nasa.