Cutar Ebola
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Shiri na uku kan Ebola

Hakkin mallakar hoto Getty

A yau za mu duba wasu daga cikin labarai irin na almara, wadanda ke kewaye da barkewar cutar.

Cutar Ebolar dai ta halaka mutane fiye da dubu daya da dari daya da ashirin a kasashen Gunea da Liberia da Saliyo da kuma Najeriya, kuma wannan adadi yana ci gaba da karuwa.

Hukumar lafiya ta majalisar dinkin duniya (WHO), da kungiyar bayar da agajin nan ta fuskar kiwon lafiya ta Medicin Sans Frontier, dukkansu sun ce barkewar cutar Ebola ta wannan karon tana da wuyar shawo kai.

Sun kuma danganta mafi yawa-yawan matsalar ce ga gibi da ake da shi wajen fadakar da jama'a da kuma bayanan da ba su kenan ba da ake bayarwa game da cutar.