Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Shiri na hudu kan Ebola

A yau za mu duba batun yadda ake yada kwayoyin cutar daga wannan mutum zuwa wancan.

Alkaluman baya-bayan nan da hukumarlafiya ta duniya ta fitar sun nuna, cewa mutane dubu daya da dari uku da hamsin ne suka halaka a halin yanzu a sanadiyyar wannan cuta ta Ebola, yayin da kuma ake samun karuwar adadin masu kamuwa da ita a kasashen Guinea da Saliyo da Liberia, ko da yake ba a sami karin ko daya a Najeriya ba.

A zancen da ake yanzu dai, kasar Liberia ce ke da adadi mafi yawa na wadanda wannan cuta ta halaka.

Sai dai shugabar kasar, Ellen Johnson Sirleaf, ta bayar da sanarwar wasu tsauraran matakan shawo kan matsalar, wadanda suka hada da kafa dokar hana fita, da killace wadanda ake ganin sun kamu da cutar, da kuma rufe hanyoyin shiga wasu wurare biyu na babban birnin kasar, Monrovia, ciki kuwa har da wata babbar unguwar masu karamin karfi, duk dai a kokarin shawo kan matsalar yaduwar cutar.

Ga dai AbdusSalam Ibrahim Ahmed da karin bayani.