Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya 23/08/14

Masu iya magana kan ce, " Babu nakasasshe , sai kasasshe! Ma'ana, dukkan larurar da ta fada wa mutum, idan ya tashi tsaye yana iya daukar matakan da zai iya ganin bayanta.

A kan haka ne Ahmad Abba Abdullahi ya tattauna da wani matashi, Malam Isiyaku Adamu Gombe, wanda makaho ne, wanda kuma ya kammala karatun digirinsa na biyu a nan Birtaniya.

Malam Ishiyaku, shi ne sakataren kungiyar makafi ta kasa a Nijeriya, sun kuma tattauna ne kan irinkalubalen da ya fuskanta , kafin kaiwa ga wannan matsayi da ya samu kansa.