Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Shiri na biyar kan Ebola

A yau za mu duba matakan da suka kamata a bi don kaucewa kamuwa da cutar Ebola.

Ya zuwa yanzu dai kusan mutane dubu daya da dari biyar ne suka rasa rayukansu a sakamakon cutar ta Ebola.

Galibin mutanen kuma sun rasu ne a kasashen Laberia da Guinea da Saliyo, koda yake cutar ta isa Nigeria.

A wannan makon Jumhuriyyar Dimokuradiyyar Congo ta kasance ta biyar cikin kasashen da aka tabbatar da bullar cutar ta Ebola, amma dai ba a kai ga tabbatar da wasu bayanai da suka alakanta lamarin da barkewar cutar a yankin Afirka ta yamma ba.

Ga dai AbdusSalam Ibrahim Ahmed da karin bayani.