Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Shiri na shida kan Ebola

A yanzu dai mutane fiye da dubu daya da dari biyar ne suka rasa rayukansu, a sakamakon kamuwa da cutar ta Ebola a wasu kasashe hudu na yankin Afirka ta yamma.

Galibin mace-macen kuma sun auku ne a kasashen Liberia da Guinea da kuma Saliyo, kuma an sami tabbacin wasu mutane sun kamu da cutar a Najeriya.

A yau kuma za mu duba bayanai na kiwon lafiya ne, game da matakan gaggawa da gwamnatoci suka dauka a wannan lokaci da ake fama da barkewar cutar ta Ebola.

Ga dai AbdusSalam Ibrahim Ahmed da karin bayani.