Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

BBC Hausa Talabijin

Daga ranar Litinin, 8 ga watan Samtumbar, 2014 sashen Hausa na BBC zai fara gabatar da labaransa ta kafar talabijin, a wani abu da shi ne irinsa na farko ga tashoshin watsa labarai na duniya.

Shirin labaran BBC Hausa a Talabijin na minti 10, zai rika kawo labaran Afirka da ma na kasashen duniya ga masu kallo ta tashar Capital TV da ke Kaduna a Nigeria da kuma tashar tauraron dan adam da ke Afirka ta yamma ta Adom TV.

Za a rika gabatar da shirin ne a ranakun mako wato Litinin zuwa Juma'a, zai kuma dinga gudana kai tsaye a shafin intanet na bbchausa.com.

Sabon shirin labaran Talbijin na sashen Hausa na BBC, kari ne a kan shirye-shiryensa na rediyo, da intanet da kuma ta hanyar wayoyin salula.