Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

The Good Ones: Nagartattun mawakan Rwanda

The Good Ones wata kungiyar mawaka ce ta mutane hudu daga Rwanda. Lokacin da mawaki kuma marubucin wakoki Adrien Kazigira ya yanke shawarar kirkirar kungiyar mawaka, ya nemi hado kan "nagartattun mutane", wato mawakan da suka fi nagarta. Daga cikin sauran mutane ukun da yake wasa da su yanzu, daya karamin manomi ne kamarsa, daya direba ne, daya kuma malamin makaranta. A Rwanda, galibi sun fi yin wasa a karshen mako a wuraren daurin aure ko jana'iza.

Da jita kwalli daya, da kuma wasu kayan kida da muryoyi, su kan samar da sauti mai jan hankali na gargajiya kuma na zamani a lokaci guda. Wakar 'Eudia', wacce suka rera don BBC Africa Beats, daya ce daga cikin wakokin soyayyar da Adrien ya rubuta wa mai dakinsa bayan mutuwarta.

A shekarar 2009 Ian Brennan, wani mai shirya wakoki na Amurka wanda ya taba cin kyautar Grammy, ya gano su, sannan ya nadi wakoki goma sha biyun dake album dinsu na farko mai suna Kigali Y' Izahabu a dare daya a gidan wani abokinsa. A watan Yulin shekarar 2014 suka fita daga Rwanda a karo na farko, lokacin da suka yi wasa a bikin Womad a Burtaniya--wasan da ya kayatar da dimbin 'yan kallo.