Matasan da suka dogara kaco kan a kan Internet

Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa matasa da dama na matukar amfani da shafin internet fiye da kima.

Binciken da aka yi a kan matasa dubu daya da dari uku ya gano cewa kashi 16 cikin dari na matasa masu shekaru 18 zuwa 25 na amfani da shafukan internet fiye da kima.

Kusan kashi 16 cikin dari sun amince da cewa su kan shafe sa'oi 15 a kowace rana a shafin internet.

Binciken ya duba alamomi biyar da masu fama da wannan matsala kan nuna

Na farko shi ne su kan shafe sa'oi kan shafukan internet

Na biyu sukan fusata a duk lokacin da aka yi masu magana yayinda da suke amfani da shafin internet.

Na uku su kan kebe kansu daga iyali kuma hankalinsu kan tashi a duk lokaci da aka samu tangarda a layin sadarwa.

A cikin wata takarda da aka wallafa a makon da mu ke ciki a mujjalar addictive Behaviours, Dr Andrew Doan ya bayana cewa a ganinsa akwai masu fama da wannan matsala.

Ya ce ya rika amfani da tabaraun google glass har na sa'oi 18 a kowace rana kuma har dabiar ta soma koma masa jiki.