Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Mawakiya Lala Njava

Mawakiya Lala Njava ta fitar da sabon faifan bidiyon salon wakarta Malagasy Blues. Ta gaji waka a wajen iyayenta. Lala ta yi wakar hadin gwiwa tare da 'yan uwanta Pata da Dozzy Njava da kuma Christian Ravalison. Lala na zaune a birnin Brussels tare da 'yan uwanta kuma ta na bada kyuatar wani bangare na kudin da take samu daga sayar da faya-fayen wakokinta.