Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Yadda na kubuta daga hannun Boko Haram

A Najeriya, bayan watanni shida da kungiyar Boko Haram ta sace fiye da 'yan matan Chibok 200, BBC ta tattauna da 'yan mata uku da suka samu kubuta daga hannun kungiyar ta Boko Haram.

Gwamnatin Najeriyar dai ta ce ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da kungiyar ta Boko Haram, kuma ana sa ran yarjejeniyar za ta kaiga sako sauran 'yan matan Chibok din dake hannun 'yan kungiyar.