Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya 08/11/14

Jihar Yobe na daya daga cikin jihohi ukku da matsalar tsaro ta sa gwamnatin Najeriya ta sa wa dokar ta-baci, a sakamakon hare haren 'yan Boko Haram.

Wasu dai na danganta rashin tsaron da matsalar rashin aikin yi.

Gwamnatin jihar Yoben yanzu ta bullo da wani shiri na tallafa wa matasan da suka kammala karatun diploma, ta hanyar koya masu sana'o'i da kuma kirkiro da guraben aikin yi.

Alhaji Muhammad Kati Machina, wani tsohon babban sakatare da yayi ritaya a jihar, shi ne aka damkawa shugabancin wannan kwamiti;

Kuma yayin wata ziyara a nan sashen Hausa na BBC inda ya tattauna da Ahmad Abba Abdullahi game da irin ayyukan da suke gudanarwa