Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Bam ya hallaka mutane 47 a Potiskum

Akalla mutane arba'ain da bakwai ne suka hallaka, a wani harin bam da aka kai a kan wata makarantar Sakandare dake Potiskum na jihar Yoben Najeriya. 'Yan sanda sun ce wani dan kunar bakin wake ne da ya saje cikin dalibai, ya kai harin, kuma galibin mamatan 'yan makaranta ne. Ya zuwa yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kai harin. Ga Aichatou Moussa da karin bayani: