Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Dokar ta-baci a wasu jihohin Nigeria

A Najeriya yayin da takaddama ta kaure game da fa'ida ko illar tsawaita wa'adin dokar ta-baci a jihohin Borno da Yobe da Adamawa da ke shiyyar arewa-maso-gabashin kasar, inda rikicin boko haram ya fi kamari, wasu masu fada a ji na ganin cewa kamata ya yi jama'a su shiga shirin kare kansu da kansu, sannan kuma a shigar da maharba da 'yan kato-da-gora cikin harkar tsaron dumu-dumu.

Shin wace riba ko illa za a iya cewa dokar ta-bacin ta haifar?

Mene ne ra'ayinku a kan batun kare-kai?

Wadannan na daga cikin batutuwan da za mu tattauna a filin ra'ayi-riga