Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Kokarin boye litattafan tarihi a Timbuktu

Birnin Timbuktu na Arewacin Mali, ya yi fice saboda dubban tsofaffin litattafan da ke ajiye a birnin, wadanda suka shafi tarihi da shariar musulunci da kiwon lafiya da kuma ilimin sanin taurari. Sai dai masu fafutikar Islama da suka kama birnin a 2012, sun lalata litattafai masu daraja da yawa amma mazauna birnin sun tashi tsaye domin kare wasunsu. Ga rahoton Aichatou Moussa