Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Babban albishir kan yaki da malaria

Hukumar lafiya ta duniya ta yi babban albishir game da yaki da zazzabin cizon sabro - ko malaria. A rahotonta na shekara-shekara, hukumar ta ce, tun shekara ta dubu biyu, yawan mutanen da zazzabin ke kashewa ya ragu da rabi - watau fiye da mutane miliyan hudu kenan. Bari mu duba alkalumman, musamman game da nahiyar Afirka: A bara, malariar ta hallaka mutane dubu dari biyar da ashirin da takwas. A yankin Afirka na kudu da hamadar Sahara, yawan mace-macen ya ragu da kashi hamsin da hudu cikin dari, tsakanin dubu biyu da dubu biyu da sha uku. Kusan rabin mutane masu yiwuwar kamuwa da zazzabin suna da gidajen sabro. Kashi saba'in bisa dari na marasa lafiya na samun magani a cibiyoyin lafiya, amma ba kullum ba ne kananan yara ke samun zuwa asibiti. Daga karshe, tsakanin dubu biyu da dubu biyu da sha uku, kashi arba'in da uku cikin dari na mata masu juna biyu, ba su sami magungunan rigakafi ba. To domin jin yadda lamarin yake a Najeriya, wakilinmu Ishaq Khalid ya tuntubi Dokta Hassan Muhammad Garba, wani likita a Bauchi