Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Koma baya a harkar yawon bude ido a Botswana

Kasar Botswana dai na da namun daji masu yawa da kuma filaye masu fadin gaske inda dabbobin ke kiwo. Hakan ya sa 'yan yawon bude ido na kasashen waje na zuwa kasar domin duba namun dajin. Yanzu irin wannan hakar yawon bude ido ta zama hanya ta biyu ta samun kudaden shiga ga kasar, bayan harkar lu'ulu'u. Ga rahoton Aliyu Abdullahi Tanko.