Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Shekaru 10 da afkuwar guguwar Tsunami

Mummunar igiyar ruwa ta Tsunami da ta afka ma kudancin Asiya, shekaru goma da suka wuce, ta kasance daya daga cikin bala'o'i mafi muni a tarihi. Daya daga cikin yankunan da bala'in ya fi kamari, shi ne lardin Aceh na Indonesia inda wakilin BBC, Andrew Harding ya gaana da wata yarinya marainiya. Wakilin namu ya koma yankin a kwanan nan domin gaano ta. Ga dai Isa Sanusi da karin bayani.