Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Matsalar baiwa Mata da Nakasassu dama a siyasa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tamburan Jama'iyun PDP da APC na Najeriya

Saura kasa da watanni biyu a gudanar da zabukan 2015 a Najeriya.

Sai dai kuma, har yanzu, wasu bangarori na al'umma na korafin cewa ba a yi musu kyakkyawan tanadi don taka rawar da ta kamace su a tsarin zabe ba balle a fagen shugabancin al'umma.

Sai yaushe ne za a fara damawa da wasu bangarori na al'umma a lamuran zabe, kuma me ya kamata a yi don a baiwa kowa damar taka rawar da ta dace?

A ci gaba da kawo muku shirye-shiryen na musamman a kan zabukan Najeriya; mun je birnin Bauchin Yakubu inda muka dauko muku muhawarar da jama'a suka tafka a kan wadannan batutuwa

Wannan shi ne abunda muka tattauna a Filin Ra'ayi Riga na wannan makon.