Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Na ba da shawara a jinkirta zaben Nigeria - Dasuki

Mai bayar da shawara akan harkokin tsaro a Nigeria ya yi kira ga hukumar zaben kasar da ta jinkirta zaben kasar da za a yi a wata mai kamawa, domin ta sami isasshen lokacin rarraba katunan zabe ga mutanen da suka cancanci kada kuri'a.

Wannan kira ya zo ne a yayin da Shugaban kasar Goodluck Jonathan yake fuskantar babban kalubale a zaben daga dan takarar jam'iyyar hamayya ta APC, Janar Muhammadu Buhari.

A lokacin da ya ke magana a cibiyar gudanar da bincike ta London, watau Chatham House, Kanar Sambo Dasuki Mai Ritaya, ya ce har yanzu ba a kai ga rarraba katuna milyan talatin ga masu su ba a duk fadin Najeriya, babu kuma ma'ana a yi zaben ba tare da an rarraba ba.

Editan sashen Hausa Mansur Liman ya tambayi Mai bayar da shawara kan harkokin tsaron na Nigeria, Malam Sambo Dasuki, ko a ganin shi, akwai isasshen tsaro a Nigeriar da za a gudanar da zabe?