Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Jinkirta zabe ba zai sa mu karaya ba, in ji Buhari

A Najeriya, dan takarar shugabancin kasar a inuwar Jam'iyyar APC Janar Muhammadu Buhari, ya ce dage zabubukan kasar da aka yi shi ne na karshe da kundin tsarin mulkin kasar ya yarda da shi.

A martaninsa na farko tun bayan bayar da sanarwar dage zabukan a daren assabar, Janar Buhari ya shaida wa wani taron manema labarai da ya kira a Abuja da yammacin jiya cewa kodayake dage zaben bai yi musu dadi ba, wannan sam bai sa suka karaya ba.

Haruna Shehu Tangaza ya halarci taron manema labaran ga kuma rahotonsa.