Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

2015: Sarki Muhammadu Sanusi ya gargadi jami'an tsaro

Mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi Na-Biyu, ya yi kira ga hukumomi da 'yan siyasa da su guji yin abin da zai iya haddasa fitina a kasar.

Ya fadi hakan ne bayan dage zaben da aka shirya yi a kasar zuwa watan Maris.

A tattaunawar da ya yi da wakilimmu Yusuf Ibrahim Yakasai a Kano, sarkin ya ce ya yi mamaki a ce jami'an tsaron Najeriya na cewa ba za su iya bada tsaro ba a lokacin zaben.