Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ya kamata mutane su guji rikicin zabe- AbdusSalam

A yayin da 'yan Nigeria ke ci gaba da tofa albarkacin bakin su dangane da dage babban zaben kasar zuwa watan gobe, a bangare guda kuma wasu tsofaffin shugabannin kasar sun gargadi 'yan kasar da kada su kuskura su bari a maimata irin kura-kuran da aka samu a baya a lokacin zabe, musamman zaben shekara ta 2011 inda aka samu mummunan tashin hankali bayan zaben.

Tsohon shugaban Najeriya Janar Abdusalami Abubakar na daga cikin shugabannin na baya bayan da suka yi wannan kira a matsayinsa na shugaban kwamitin tabbatar da zaman lafiya a zaben shekara ta 2015, wanda cibiyar Bishop Mathew Kukah ta kafa.

An dai daurawa wannan kwamitin alhakin tabbatar da yin biyayya ga yarjejjeniyar zaman lafiyar da Shugaba Goodluck Jonathan na Jam'iyyar PDP da takwaransa Janar Mohammadu Buhari na Jam'iyyar APC suka rattabawa hannu.

Mansur Liman ya tattauna da Janar Abdussalami Abubakar din gabannin sanar da dage zaben kasar, inda ya fara da tambayarsa, ko menene dalilin da ya sa ya yi wannan gargadi?