Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Lafiya ta kalau in ji Janar Buhari

Dan takarar shugabancin Nigeria na jam'iyyar APC, Janar Muhammadu Buhari ya ce lafiyarsa kalau, masu jin tsoronsa ne suke karya a kansa. A hirarsa da Aliyu Abdullahi Tanko a London, Janar Buhari ya musanta zargin cewar bai da koshin lafiya kamar yadda wasu 'yan jam'iyyar PDP mai mulkin Nigeria ke yada wa. Buharin kuma ya yi zargin cewa an dage zaben Nigeria ne saboda anga alamun shi ne zai samu nasara kuma ya ji takaicin dage zaben da aka yi tun farko.