Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Kokarin kwato birnin Tikirit daga hannun IS

Sojojin gwamnatin Iraqi sun ce sun kwace iko da larduna da dama dake kewayen Tikrit.

Mahaifar marigayi Saddam Hussein dai ta fada hannun 'yan kungiyar IS ne a bara.

Wannan shi ne farmaki mafi girma da sojojin na Iraqi ke kaiwa a birnin na Tikrit, tare da goyon bayan mayakan Sunni da dakarun sa kai na 'Yan Shia. Amurka dai ta ce ba ta da hannu a farmakin.

Ga rahoton Aichatou Moussa.