Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

INEC ta raba kashi 80 na katunan zabe

Yayinda ya rage kimanin makonni uku a gudanar da zabe a Najeriya bayan dagewar da aka yi da makonni shida, hukumar zaben kasar INEC, ta yi ta baiyana cewa ta yi cikakken tanadi na gudanar da zaben a ranar 28 ga wannan watan na Maris da kuma 11 ga watan Afrilu kamar yadda aka tsara.

Mukaddashin daraktan hulda da jama'a na hukumar zaben, Mr Nick Dazang ya shaidawa wakilinmu Abdullahi Kaura Abubakar cewa suna ganin alamun nasara a yakin da jami'an tsaro ke yi da 'yan Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya wanda zai ba da damar gudanar da zabbukan cikin nasara a fadin kasar.