Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Matsalar karancin man fetur a Nigeria

A cikin 'yan kwanakin da suka wuce matsalar karancin man fetur ta kara ta'azzara a Nigeria, abin da ya tilastawa masu ababen hawa shafe lokaci mai tsawo a gidajen mai kafin su samu. Wasu bayanai sun ce an sassanta tsakanin gwamnati da dillalan man fetur na kasar domin kawo karshen dogayen layuka a gidajen mai. Wace irin matsala wannan karancin mai ya haddasa muku ? Wace hanya za abi domin kaucewa irin wannan matsala a nan gaba? Maudu'inmu kenan na yau a filin Ra'ayi Riga.