Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Simone Gbagbo za ta sha daurin shekaru 20

Kotu a Ivory Coast ta yanke wa Simone Gbagbo - uwargidan tsohon shugaba Laurent Gbagbo - hukuncin daurin shekaru ashirin, bayan an same ta da laifi a tashin hankalin da ya biyo bayan zaben shugaban kasa na dubu biyu da goma. Kusan mutane dubu uku ne suka hallaka a fadan da ya barke, bayan da mista Gbagbo ya ki amincewa ya sha kaye. Ga rahoton Isa Sanusi: