Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya 14/03/15

A kwanakin baya ne aka yi bikin ranar karanta littafi ta duniya.

Kasashe fiye da dari ne ke yin bikin a kowace shekara, wadda, a wannan shekarar, aka kebe da nufin karfafa gwiwar yara domin su rika karanta littafai.

A Najeriya dai, kamar wasu kasashen da ke tasowa, ana fuskantar koma-baya game da karance-karance.

Malam AbdulAzeez AbdulAzeez, wani marubuci ne a Nigeria, kuma a filinmu na Gane Mani Hanya na wannan makon, ya soma da yi wa Nasidi Adamu Yahaya bayani kan muhimmancin wannan rana: