Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

'Za mu ga bayan Boko Haram'

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, ya ce ya yi amannar 'yan matan Chibok da kungiyar Boko Haram ta sace suna nan da ransu, kuma za a gano su. Sannan nan da wata guda za a ga bayan 'yan Boko Haram din. Shugaba Jonathan yana bayyana hakan ne a hira da BBC, mako guda kafin babban zaben kasar, wanda ya ce shi ne zai sake lashewa.