Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya 21/03/2015

Hakkin mallakar hoto
Image caption Goodluck Jonathan ya bayar da tabbacin cewa za a kwato illahirin yankunan da 'yan kungiyar Boko Haram suka mamaye a kasar.

Yayin da ya rage mako daya daidai a gudanar da babban zabe a Najeriya, Shugaban kasar, Goodluck Jonathan, ya bayar da tabbacin cewa za a kwato illahirin yankunan da 'yan kungiyar Boko Haram suka mamaye a kasar.

Sannan kuma ya baiyana sirrin da ya sa gwamnatinsa ta fara samun nasara a cikin dan kankanen lokaci wajen murkushe Boko Haram.

Shugaban ya kuma yi kurarin cewa zai lashe zaben dake tafe duk da tsananin adawar da ya ke fuskanta. Sai dai ya ce a shirye yake ya rungumi kaddara, idan har ya fadi zaben.

Shugaban ya yi wadannan kalaman ne a wata hirar da yayi da wakilin BBC Will Ross. Ga fassarar hirar da suka yin: