Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Sojoji sun kawar da 'yan Boko Haram daga Alagarno

Rundunar sojan Nigeria ta ce dakarunta sun fatattaki mayakan kungiyar Boko Haram daga dajin Alagarno a jihar Borno. Dajin na Alagarno na daga cikin wuraren da ake cewa mayakan na da sansanoni mafiya girma baya ga na Sambisa. Wakilinmu Ahmad Abba Abdullahi ya tuntubi Kanar Sani Usman Kukasheka, mukadashin kakakin rundunar sojan kasa na Nigeria domin jin karin bayani.