Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Taba Kidi Taba Karatu 05/04/2015

A daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan yiwuwa ko akasin haka, na dacewar hukuncin kisa a sassa daban daban na duniya, wani abu da ke jan hankali a kasashe musamman masu tasowa shi ne yadda mutane ke shafe shekara-da-shekaru a gidan yari suna jiran tsammani kan hukuncin da aka yanke musu - a mafiya yawan lokuta na kisa.

Wani mutum da ya tsallake rijiya da baya shi ne THANK- GOD EBESSI - wanda ya shafe shekaru ashirin a gidan yari yana jiran a yanke masa hukuncin kisan da alkali ya zartar masa, bayan da aka same shi da laifin fashi da makami a Nijeriya.

Sai dai ya samu kansa bayan da kungiyoyin kare hakkin bil'adama suka shiga cikin lamarin nasa.

Mr Ebessi - wanda dan asalin jihar Edo ne a Nigeriar, a filinmu na Taba Kidi Taba karatu na wannan makon ya yiwa Naziru Mikailu karin bayani kan halin da ya samu kansa: