Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

An kama fitaccen dan adawa a Burundi

An kama wani fitaccen mai fafutikar kare Hakkin Bil-Adama a Burundi yayinda jama'a ke ci gaba da zanga-zanga a rana ta biyu a jere, domin nuna adawa da matakin shugaba Pierre Nkurunziza na neman wa'adin mulki na uku. An tsare Pierre Claver Mbonimpa ne, bayan ya yi hira da wani gidan rediyo mai zaman kansa, wanda tuni hukumomi suka rufe. Akalla mutane 4 ne aka kashe kawo yanzu. Ga rahoton Aichatou Moussa.