Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ana ci gaba da aikin ceto a Nepal

Akalla mutane dubu biyar ne aka tabbatar sun hallaka, a sakamakon girgizar kasar da ta afka wa Nepal a ranar Asabar. Wasu karin mutanen fiye da dubu shidda da rabi kuma sun jikatta. Ana ci gaba da aikin ceto a cikin Khatmandu, babban birnin kasar, amma a wajen birnin har yanzu ana kokarin cimma yankuna masu tsaunika inda bala'in ya fi muni. Ga rahoton Aminu Abdulkadir