Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Sojoji sun ceto mata 293 daga dajin Sambisa

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta ceto 'yan mata 200 da kuma manyan mata guda 93 a lokacin da dakarunta suka kai samame a dajin Sambisa.

Kakakin rundunar sojin kasa na kasar, Kanal Sani Usman, ya ce binciken da suka yi ya nuna cewa babu 'yan matan Chibok a cikin matan da aka ceto.