Jonathan ya jagoranci taron majalisar kasa na karshe

Hakkin mallakar hoto State House
Image caption Tsofaffin shugabannin Nigeria da Shugaba Jonathan

Dukkanin tsofaffin shugabannin Nigeria sun halarci taron majalisar kasa a Abuja, wanda ake ganin shi ne na karshe da shugaba Goodluck Jonathan zai jagoranta.

Shugaban kasa mai jiran gado Janar Muhammadu Buhari ya halarci taron, tare da Janar Olusegun Obasanjo da Janar Yakubu Gowon da Alhaji Shehu Shagari da Janar Ibrahim Babangida da Abdulsalami Abubakar da kuma Cif Ernest Shonekan.

Galibin gwamnonin kasar sun halarci taron inda aka yanke shawarar cewa za a nuna wa shugaban kasa mai jiran gado fadar shugaban kasa a jajibirin bikin karbar mulki a kasar.

Taron majalisar kasar ya kuma amince da kafa burtuloli na shanu domin yin kiwo da kuma kawo karshen tashin hankali tsakanin fulani makiyaya da manoma.

Majalisar kasa a Nigeria ta kunshi shugaban kasa da tsofaffin shugabannin kasa da tsofaffin shugabannin kotun koli da kuma mai ci da gwamnoni da shugaban majalisar wakilai da kuma dattijai.