Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

EU na neman taimako saboda 'yan ci-rani

Tarayyar Turai ta nemi agajin majalisar dinkin duniya, wajen tarwatsa kungiyoyin miyagu da ke fataucin 'yan ci-rani zuwa Turan, da kuma izinin lalata jiragensu a yankin ruwan Libiya. Tarayyar Turan ta kuma bukaci kowace daga cikin mambobinta da ta dauki nata kason na 'yan ci-ranin. To sai dai abin da kamar wuya a fagen siyasa. Ga rahoton Bashir Sa'ad Abdullahi.