Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya 30/05/2015

Rini na daga cikin tsofaffin sana'o'in kasar Hausa, da ya bai wa kasar ta Hausa zarafin shiga a dama da ita a harkar cinikayyar kasa da kasa daruruwan shekaru da suka gabata.

Sana'ar dai ta samu bunkasa a yan shekarun nan, inda aka zamanantar da ita, sannan bukatar kayan da ake rinawa suka kara yawaita a duniya, musamman ma dai wasu kasashen Afirka.

To sai dai a wannan karon masu sana'ar ta rini a Kano na cewa suna fuskantar barazanar dakatar da su daga sana'ar, sakamakon shiga cikinta da 'yan China suka yi, inda suke kawo runannun kaya daga kasar su suna sayarwa a Najeriya.

Wakilinmu Yusuf Ibrahim Yakasai ya duba mana wannan batu, ga kuma rahoto na musamman da ya hada mana.