Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Kungiyar IS na azabtar da kananan yara

Kungiyar IS na amfani da kananan yara a filayen daga a Syria da Iraki.

Wannan dai labari ne mai tayar da hankali. Kungiyar na ba yaran horo irin na soja, kuma wadanda ake zargi da hada baki da kungiyoyin hamayya ana azabtar da su, a wasu lokutan ma akan kashe su.

BBC ta dauko hotunan yadda ake azabtar da wani yaro. Ga rahoton Jimeh Saleh. Watakila, wasu hotunan za su iya tayar ma ku da hankali.