Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Tallafin abinci a Sudan ta Kudu

Shugabannin kasashen yankin Gabashin Afrika, sun yi kira ga shugabannin Sudan ta Kudu da su kara yunkurawa domin kawo karshen yaki a kasar, wanda ya hallaka mutane kimanin dubu 50.

A jawabinsa, lokacin bukukuwan ranar samun 'yancin kan Kenya, shugaban Uhuru Kenyatta, ya gargadi 'yan siyasar Sudan ta Kudun, da kada su ba al'ummominsu kunya.

Kiran dai ya zo ne yayinda Hukumar abinci ta duniya, ta ce mutane kusan miliyan 4 da rabi a Sudan ta Kudun za su bukaci agajin abinci a cikin 'yan watanni masu zuwa.

Ga rahoton Aminu Abdulkadir.