Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

'Ina son in zama shugabar Somalia'

Fadumo Dayib, wata 'yar Somalia, ta ce ba abin da zai hana ta yin takarar shugabancin kasar a badi.

Ta girma a matsayin 'yar gudun hijira a kasashen Kenya da Finland, inda ta koyi karatu da rubutu tana da shekara sha hudu.

Ta kuma sami digiri kala-kala a kan kiwon lafiya. BBC ta zanta da ita bayan ta kammala karatu a jami'ar Harvard a Amirka: