Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Samar da makamashi daga dagwalon mahauta

To ko kun taba tsayawa ku yi tunanin yaya ake yi da dattin mayanka? A Uganda an dade ana ina-za-a saka da dagwalon, saboda gudun gurbatar muhalli. Sai dai a yanzu masana kimiyya na taimaka wa wata mahauta a birnin Kampala, wajen sarrafa jinin da sauran dattin, zuwa makamashi. Wasu 'yan kasuwa kuma, kakarsu ta yanke saka. Ga dai rahoton Jimeh Saleh