Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Za mu yi maganin Boko Haram - Issoufou

Shugabannin kasashen yankin tafkin Chadi da Benin sun ce dakarun rundunar hadin-gwiwarsu za su fara aikin fatattakar Boko Haram a karshen watan Yuli. A sanarwar bayan taron da suka fitar a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, shugabannin kasashen biyar sun sha alwashin bayar da $30m domin samarwa dakarun makamai da sauran kayan aiki na yaki da kungiyar ta Boko Haram. Ga karin bayanin da shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar ya yi wa manema labarai