Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Taba Kidi Taba Karatu 14/06/15

A Najeriya, sannu a hankali tsoffin mawaka na al'ummar Ibo da ke kudu maso gabashin kasar, wadanda suka shahara a fagen wakoki da kade-kade na gargajiya da na zamani irin su Sir Warrior da Cif Osita Osadebe, suna ta gushewa. Amma yanzu ana samun matasa da ke maye gurbinbsu, ko da yake sabbin jinin sun fi mayar da hankali ne ga kade-kade da wakokin zamani irin na hip-hop. A filinmu na ''Taba Kida Taba Karatu'' na yau za mu leka wajen wakilinmu a Enugu, AbdusSalam Ibrahim Ahmed, wanda ya zanta da daya daga cikin ire-iren matasan da ke tasowa a yankin na kudu maso gabashin Najeriya, mai suna Caxton Chukwudi Anokwuru.