Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Mahawara kan azumi a Biritaniya

Yayin da a wannan makon ake shirin soma azumin watan Ramadan, wani malami a nan Biritaniya ya ba da shawarar a rage yawan awoyin da ake kwashewa ana azumin.

Dalili kwa shi ne: rana ba ta faduwa da wuri, kuma nan da nan alfijir ke ketowa.

Wasu na ganin cewa kwashe tsawon lokaci ba ci ba sha, zai iya yin illa ga lafiyar mutum. Ga rahoton Aminu Abdulkadir: