Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya 20/06/15

A wannan makon ne Musulmi a fadin duniya suka fara azumin watan Ramadan. Watan na Ramadana dai shi ne wata na tara a jerin watannin musulunci, kuma azumin na daga shikashikan musulunci guda biyar.

A kan haka ne wakilinmu a Kano Yusuf Ibrahim Yakasai ya yi tattaunawa ta musamman da wani malamin addinin musulunci, Malam Najib Auwal Abubakar, mai koyar da darusan addinin musulunci a Jami'ar Bayero, kuma limamin masallacin juma'a da ke unguwar Rijiyar Zaki.

Ya kuma fara ne da tambayar sa ko mene ne matsayin azumin watan Ramadana?